Najeriya ta saki jerin sunayen nakassasu 23 na gasar Rio 2016
–Kwamitin wasannin nakassau ta Najeriya sun saki sunayen yan wasa 23 domin gasar
–Najeriya zatayi takara a wajen gudu, daga karfe, da ku tebur tanis
– Kwamitin wasannin nakassau ta Najeriya sun saki sunayen yan wasa 23 da zasu wakilci Najeriya a gasar Rio olymics da za’a yi a watan gobe.
Mai maganan kwamiin, Mr. Patrick Ibeh yace nakassasun zasuyi takarane kawai a wasanni guda 3, gudu, daga karfe,da kuma tebur tanis.
Mr. Ibeh ya bayyana cewa najeriya zata samu nasara a wasannin kuma kochnina 10 ne zasu raka su kasar Brazil. Wadanda zasu wakilci Najeriya a wasan gudu sune Hannah Babalola, Eucharia Iiazi,Laurettea Onye,Lovina Onyegbule da Flora Ugwunwa,yayinda Friday Aibange na kacal namiji a cikinsu.
Wadan zasu wakilci najeriya a wasan daga karfe sune Nsini Ben, Lucy Ejike, Ndidi Nwosu, Bose Omolayo, Josephine Orji, Esther Onyema da Latifat Tijani a bangaren mata. A bangaren maza kuma sune Yakubu Adesokan, Roland Ezuruike, Abdulazeez Ibrahim, Nnamdi Innocent, Opeyemi Jegede, Paul Kehinde da Tolu-lope Taiwo
KU KARANTA : Rawar da Nigeria ta taka a gasar Olympics 2016
Zaku tuna cewa nakassasun najeriya sunci kyautar zinariya 6, azurfa 5 da kuma tagulla 2 a wasan Rio daya gabata a London 2012.
Asali: Legit.ng