Yadda Ali Modu Shariff ya haddasa rikicin Boko Haram
Babban mai gabatar da kara na jihar Borno ya bayyana yadda halayar Ali Modu Shariff ta taimaka wajen samar da kungiyar Boko Haram a jihar, ya kuma tambayi dalilin da ya sa tsohon gwamman ya nemi gafarar’yan Boko Haram din a shekarar 2011
Kwamishinan Shari’a kuma babban mai gabatar da kara na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan ya ce, dagawa da bukatar dawwama a mulki ne suka haifar da kungiyar Boko Haram a jihar Borno
Kwamishinan shari’an ya bayyana hakan ne a yayin wani babban taro na kungiyyar Lauyoyi ta kasa wanda aka yi a Fatakwal, ya kuma dora laifin alhakkin kisan shugaban ‘ya Boko Haram Mohammad Yusuf a kan Modu SHariff yana mai cewa, “me Modu shariff ya yi a matsayinsa na babban jam’in tsaro na jihar, me ya sa ba a kyale Muhammad Yusuf yayi jawabi ga ‘yan sanda ba”.
Sannan Barisata Kaka ya cigaba da cewa, a ranar 5 ga watan Yuli Ali Modu Shariff ya nemi gafarar ‘yan kungiyar a bisa wani liafin da ya yi musu, ko me yasa ya nemi gafarararsu idan babu rami mai ya kawo maganar rami?
Baristan ya kuma kara da cewa, jami’an tsaro sun kashe ‘yan kungiyar su 17 amma gwamnatin Modu Shariff ba ta yi Tir da kisan ba, ba ta fitar da wata sanarwa ba ko ta jajanta abinda ya faru, ta kau da kai tare da yin shiru kamar bai faru ba, “masu lura da al’amura, da kuma wasu a gwamnatinsa sun ba shi shawara da cewa, yin shiru ga lamarin zai iya janyo matsala…”
“… ‘yan kwanaki a tsakani a hirarsa da Jaridar Daily Trust, Muhammad Yusuf ya yi alkawarin daukar fansa domin shirun da gwamnatin jihar ta yi, na nuna cewa shiri ne na ganin bayan mutanensa….” Bayan ‘yan kwanaki da yin hakan Shugaban ya kaddamara da yaki da gwamnatin tarayya ya kuma umarci jama’arsa da su dauki makamai
Asali: Legit.ng