Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)

Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)

‘Yan arewa sun iya daukar wanka a cewar Temitope Popoola ta Legit.ng, don haka ta zabo wasu samari ‘yan kwalisa da suka dau wakan colabo da suwaga har da ma da na fitted cikin har da wasu ‘yan fina-finan Hausa.

Muna gabatar muku da wasu samari ‘yan kwalisa daga arewacin kasarnan daga tsatson Hausa Fulani, don ku sani cewa ba duk wanda ku ka hadu da shi a kudu yana aikin wahala ko na kaskanci ba, ku dauke shi a matsayin baya ga dangi a Najeriya.

Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)
Adam A Zango: mawaki mai shiryawa da kuma fitowa a fina-finan Hausa

Adam A Zango: Mawaki mai shiryawa da kuma fitowa a finan Hausa, fina-finansa da wakokinsa na jan hankali masu kallo musamman matasa. Ya taba janyo ka-ce-na-ce a tsakanin matasa sakamakon wani furuci da yayi na cewa yafi matasan wata jiha a arewa iya daukar wanka, wanda hakan ya sa suka yi caaa a kansa, ko hakan ta tabbata ke nan da sa dan wasan a jerin matasa 'yan kwalisa daga arewa na Legit.ng?

Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)
Yakubu Mohammed ko Mallam Yax

Yakubu Mohammed: Na hannun daman Sani Danja, kuma Mawaki, mai shiryawa da fitowa a fina-finan Hausa, Malam Yax kamar yadda ake kiransa, yanzu za a ce ya karkata ga fitowa a fina-finan da ke yi a kudancin kasar watau Nollywood, bayan ga fitowa a salon wakokin na zamani da  'yan kudun. Dan asalin jihar Plato, shi ya lashe kyautar jarumin jarumai daga Arewa na City People Entertainment award na shekarar 2015.

Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)
Misra Yax da kyautarsa ta City People

KU KARANTA: Hana fim village a Kano kwangilar malamai ce 

Zabi ki darje ‘yan kwalisa daga arewa (Hotuna)

SadiqSani Sadiq daya daga cikin taurarin fina-finan hausa

Sadig Sani Sadiq: Jarumin jarumai na Kannywood Awards da shima ya cinye a wannan shiga na zabi ki darje daga arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng