Wata ya taba rabuwa gida biyu a tarihin duniya
-Wata ya taba rubuwa gida biyu a tarihin duniya
-Wasu hotuna daga Hukumar NASA sun tabbatar da faruwar hakan
-Hakan ya taba faruwa a tarihin musulunci
Wasu hotuna da Hukumar Kula da sararin Samaniya ta Amurka NASA ta wallafa wanda kuma yada a duniya ya nuna cewa, hakika wata ya taba rabuwa gida biyu, sannan ya koma ya hade, hotunan da jiragen jigila zuwa sararin samaniya na kumbo Apollo 10 da kumbo Apollo11 wadanda Hukumar NASA ta harba zuwa duniyar Wata sun aiko da hotunan da suka wata alamar tsagewar watan wadanda ke tabbatar da cewa, ya taba rabuwa gida biyu a baya.
Rahoton Hukumar binciken ta Amurka a bisa hujjoji na kimiyya daga wasu sassa na duniya da dama, sun ce hotunan da ke nuna tsagewar Wata, ya tabbatar da cewa hakika ya taba rabuwa gida biyu a wadansu shekarun baya a tarihin duniyar watan.
Rahoton yace masana kimiyya sun kasa bayar da bayanin dalilin da ya sa Watan ya rabe biyu, saboda hakan a bisa saninsu na kimiyyar halittun sarrarin samaniya, bai taba faruwa ba ga kowacce irin halittar Ubangij a samaniya, kafin wanda suka gani a tare da Watan, sun kuma kara da cewa, wannan alamar tsagewa, ba zai taba samuwa a jikin watan ba, in ban da cewa ya taba rabuwa gida biyu, sannan ya koma ya hade.
A cewar wasu Malaman Musulunci, rabuwan Wata, ya faru ne a bisa umarnin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a garin Makka a lokacin da kafirai suka nemi da ya yi hakan domin su yarda da shi. Kuma ya zo a cikin Al Qur’ani a suratul Qamar 54:1
Asali: Legit.ng