Girgizan kasa ya kashe sama da mutane 240 kasar Italiya
Gine gine da dama sun tsatsatsage biyo bayan wani mummunan girgizan kasa da ya auku a kasar Italy a ranar Laraba 24 ga watan agusta wanda yayi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama.
Mutane da yawa ne ake ganin girgizan ya rutsa dasu cikin dago dagon gidaje da suka rushe a yankunan Amatrice, Accumoli da Pescara del Tronto inda bala’in yafi kamari.
Masu bayar da agajin gaggawa sama da dubu 4000 dauke da manyan kayan aiki ne suka yi yunkurin ceto mutanen, amma dole suka dakata saboda ragowar gidajen dake rushewa.
Masu bayar da agajin sun baiwa yan jaridu da masu kallo shawarar su tashi daga Amatrice ga gaggawa saboda garin na shirin rugujewa gaba daya, inji wakilin BBC. Rahotanni sun nuna yawancin wadanda abin ya shafa kanana yara ne. sa’annan an samu labarin mutane 184 ne suka rasu a garin Amatrice, 64 a Arquata da 11 a Accumoli.
A yanzu haka mutane 264 suna asibiti, daya daga cikin wadanda suka sha a garin Amatrice yace “muna cikin barci a mota sa’adda kasar ke girgiza, daga nan ne mafi munin girgizan ya afku sai motar ta fara motsawa tana tafiya”. Shugaban yan bada agajin Macerata Gianni yace sun ceto wani kare daga bala’in, kuma bai damu ba ko kare ne ko mutum ne, su dai sunyi aikin su.
A yanzu dai shugaban kasar Italiya Matteo Renzi ya jagoranci wata zaman gaggawa na majalisar sa inda suka yanke shawarar sake gina garuruwan da abin ya shafa, da kuma samar da sansanin wucin gadi ga yan gudun hijiran.
Da yammacin ranar laraba 24 ga watan agusta aka hako wata karamar yarinya daga cikin sauran wani gida daya rushe bayan ta kwashe awanni 17 a kauyen Pescara del Toronto.Acewar BBC, masu bayar da agajin sunce sun hako gawawwakin mutane biyar daga ginin otel din Roma daya ruguje wanda kafin rugujewarsa mutane 70 ne a ciki.
A lokacin da girgizan ya faru, girgizan farko ya kai ma’auni 6.2 ya kai nisan kilomita 10 a cikin kasa. Shima paparoma jon pol ya jajinta ma wadanda abin ya shafa.
Asali: Legit.ng