Farashin buhun shinkafa zai sauko N9000 kafin watan Disamba- inji jigon APC

Farashin buhun shinkafa zai sauko N9000 kafin watan Disamba- inji jigon APC

Ana sa ran farashin buhun shinkafa dake N18,500 a yanzu zai sauka zuwa N9000 kafin karshe shekara a cewar wani shugaban jam’iyar APC na karamar hukumar Alimosho dake jihar Legas Ganiyu Quadri.

Ganiyu ya fadi hakan ne yayin da yake karban bakontan tawagar kungiyar rotary na Akowonjo karkashin jagorancin shuwagabanninta Patrick Ikheloa da Shola Abidakun. Ganiyu ya ba da tabbacin hadin gwiwar da gwamnatin jihar Legas ta shiga da gwamnatin jihar Kebbi suka shiga na harkar shinkafa zai sanya farashin shinkafar ya sauko kasa a yankin kudu maso yammacin kasarnan.

Farashin buhun shinkafa zai sauko N9000 kafin watan Disamba- inji jigon APC

Jigon jam’iyar APC ya bayyan cewa gwamnatin jihar Legas zata kara kaimi kan harkan noma don ganin an samar da isashshen abinci a fadin jihar gaba daya. “zuwa karshen shekara, ko farkon shekara mai zuwa, za’a ga canji a jihar Legas. Tuni mun shiga hadin gwiwa da gwamnatin Kebbi.

“Mun samu manyan gonakin noman shinkafar, kuma muna sa ran motocin dakon kaya dauke da shinkafar zasu fara shigowa nan bada dadewa ba.“don haka ina baku tabbacin cewa kafin karshen shekara, farashin shinkafa zai sauka daga N18000 zuwa N9000”.

Sai dai Ganiyu ya koka da halin karancin kudade da kananan hukumomin suka tsinci kansu a ciki. Yace daya daga cikin ayyukan shuwagabannin kananan hukumomi shine biyan basussuka da ake bin kananan hukumomin.

A yan kwanakin nan bincike ya nuna farashin shinkafa ya karye a kasuwannin Hadejia na jihar Jigawa. Kamfanin dillancin labarai ta ruwaito cewa farashin ya karye ne sakamakon yawan abinci isashshe da aka samu a kasuwannin.

Binciken ya nuna a ranar talata 23 ga watan agusta a kasuwar Hadeja buhun gero ya sauko daga N18000 zuwa N14000, inda buhun shinkafa ya sauko zuwa N8500. Farashin masara da alkama ya sauko zuwa N11000 da N13000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel