Kalli wata kyakkyawar Amarya tana sumbatar Mahaifiyarta.
Shekaru da dama da suka wuce, dangantakar dake tsakanin Uwa da ‘yarta bai iya musaltuwa. Haka kuma wannan shakuwar tana kara karuwane musamman ranar auren yarinyar, bayan da amaryan da mahaifiyarta suke zubar da hawayen murna dakuma juyayin rabuwa.
Haka anan, wata Amarya mai cike da farin ciki ta tura hotonta a Instagram dinta, da hoton ke nunata tanama sumbatan mahaifitar ta a ranar aurenta, Inda tayi rubutu kamar haka “ Mama ina kyaunar ki duk ta halin da kike, Haka kuma ina kyaunar ki duk a inda kike, sannan ina kyaunarki ko ina zakije. #Uwa da yarinya sun shaku#
Abun sha’awa.
Asali: Legit.ng