Dubi kyawawan hotunan auren Obi da Ope
-Ope da Obi sunyi auren kece raini.
-Yan matan Amaryar sunyi shiga mai kayatarwa.
Ope da kyakkyawar matarsa sunyi tafiya zuwa Dubai yan satuttuka bayan baikonsu. Ma’auratan sun nuna irin soyayyar nan da a wasan kwaikwayo kadai ake ganinsu. Sun mana ba zata a hadadden auren da suka shirya. Obi ta kirashi abokin rayuwarta shi kuma Ope yace yayi sa’a da ya sameta.
Dukkan suna cikin farin ciki sun kuma sanya kaya kala daya, sun kama hannu suna nuna ma junansu soyayya a bainar ‘yan uwa da abokan arziki.
A bikin an ga yan matan amarya sunyi shiga dogayen riguna na kalar pink masu kayatarwa suma abokan ango sun mashi kara da wasu irn huluna da far-farun kaya.
Ku dubi kyawawan hotunan bikin aurensun a kasa. Cike da soyayya! Wannan baikon na Inyamuri da budurwarsa zaya baku sha’awa
Asali: Legit.ng