Yan sanda a Kano sun yiwa gidan kwankwaso kawanya
‘Yan sanda dauke makamai ne suka yiwa gidan tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso kawanya domin hana taron dauren zaurawa
Gidan wanda da ke kan titin Luguard Avenue a unguwar Nasssarawa shalkwatar kungiyar kwankwasiyya ce ta tsohon gwamnan, kuma ‘yan sandan sun killace gidan ne a bisa zargin shirin gudanar da taron daura auren zaurawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Magaji Musa Majiya ya tabbatar da ala’amarin ya na mai cewa, “mun umarci jami’anmu da su killace gidan, sakamakon wasu rahotannin sirri na shirye-shiryen gudanar da wani gangamin taron aurar da zaurawa… ‘Yan sanda ba su bayar da izinin wani taron gudanar da dauren aure ba.”
A baya dai, gwamnatin jihar Kano ta haramta kokarin yin auren zaurawan da mabiya tsohon gwamna suka shirya a filin Polo, daga baya ‘yan kwankwasiyyar suka gudanar da daurin auren a asirce a gidajen amaren a ranar Litinin.
An dai shirya rabawa amaren kayan daki a gidan gidan tsohon gwamnan kuma shalkawatar kwankwasiyyar ne da ‘yan sandan suka yiwa kawanya ranar Talata 23 ga watan Agusta, Rabiu Musa kwankwaso shi ya kikiro shirin aurar da zaurawa a lokacin yana gwamna a inda ya aurar da zaurawa sama da 1,000.
Da farko gwamnatin jihar Kano a karkashin Ganduje ta shirya auren, amma daga baya ta dakatar bisa wasu daliliai, hakan ya sa kwankwaso ya yi aniyar aurar da zaurawan 100 a filin Polo, wanda gwamnatin jihar ta hana, ta kuma soma tantance zaurawa a Hukumar Hisbah domin yin auren a wani lokaci nan gaba.
Asali: Legit.ng