Wasu fitattun ‘yan Africa da suka kafa tarihi
Ga wasu fitattun ‘yan asalin Africa da suka kafa tarihi wadanda duniya ba za a taba mantawa da su ba.
Barrack Obama
Shi ne shugaban Amurka na 44 kuma bakar fata na farko da ya taba kai wa ga wannan mukami a kasar. Mahaifisa dan Kenya ne. Wa’adin mulkinsa zai kare a watan Nuwamban 2016.
Kofi Anan
Sakaren Majalisar dinkin Duniya, kuma dan Africa na biyu ta ya taba rike wannan mukami a duniya ya na da shekaru 78 da haihuwa. Cikin abubuwan da ya yi wadanda ba za a manta da su ba sun hada da wanzar da zaman lafiya a kasashe da yawa da ke cikin rikici, da kai kayayyakin agaji.
Abubakar Tafawa Balewa
Firayi ministan farko na Najeriya wanda kuma ya karbi yancin kasar daga hannun turawan mulkin mallaka. Tarihi ba zai manta da shi ba, a lokacin da ya yi jawabinsa a majalisar Dinkin Duniya aka lakaba masa suna mai makokwaron zinare na Africa.
Usain Bolt
Dan wasan tsere da ya fi kowa gudu a duniya. Dan kasar Jamaica ne, ya kuma lashe gasar tseren mita 100 da mita 200 sau uku a jere a gasar Olympics daban-daban
Muhammad Ali
Zakaran wasan damben duniya ajin masu nauyi. Ya kuma zama gagara badau a shekarun 1960 har zuwa shekarun 1980. A shekara ta 2005 ya samu lambar shugaban kasar Amurka na waccan lokaci kuma musulmi ne mai fafutukar samun ‘yancin bakar fata a duniya.
Asali: Legit.ng