An nemi ta an rasa bayan ta bar sakon wasikar mutuwa

An nemi ta an rasa bayan ta bar sakon wasikar mutuwa

Wata mata mai suna Olubunmi Uko, mai yara uku ta bar gidanta dake yankin Fola agoro tare da daya daga cikin yaranta bayan ta bar wata wasika data rubuta, wanda a ciki take nuna zata kashe kanta.

An samu labarin matar, wadda yar kasuwa c eta bar gidanta ne a ranar laraba 17 ga watan agusta da misalin karfe 5 na safe tare da dan autan ta Seun. Da safiyar larabar ne matar ta tashi yaran nata daga barci, inda ta fada musu cewa zata kai ziyara ga wata kawarta, sai bayan ta tafi ne sauran yaran nata Iyiola da Toni suka tsinci wasikar data rubuta.

An nemi ta an rasa bayan ta bar sakon wasikar mutuwa
Olubunmi Uko

Wani dan uwan matar mai suna Folu ya fadi ma jaridar Vanguard cewa “ta rubuta wasikar ne zuwa ga yaranta, mahaifiyarta da duk wanda abin zai shafa. Tace kada wani ya bata lokacinsa wajen neman ta saboda zata je ta fada teku ne.

“tace ta gaji da wahalhalun rayuwa, tace wata kila zuwa lokacin da za’a tsinci wasikar tuni kifi ya hadiye ta. “ta dade tana kokawa da yadda kasuwancin ta ke ja baya, a dalilin hauhawan farashin dala. Tayi korafin cewa ana binta basussuka, kuma bata da halin biya.

“tace sai da taci bashin rabin miliyan don ta biya basussukan, amma daga bisani ta yanke shawarar zuba kudin cikin kasuwancin ta, da niyyar idan aka samu riba sai ta biya bashin, sai dai kash! Daga karshe kudin suka lalace a cikin harkar nata.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng