Zan kara sayo 'yan wasa - Wenger
Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ya shirya kara sayo wasu 'yan wasan tamaula kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a ranar 31 ga watan Agusta.
Wenger na shan suka kan kin sayen fitattun 'yan wasa a shekara da dama, da kuma fama da yawan rauni da 'yan kwallon Arsenal ke yi. Babban dan kwallon da Wenger ya saya a bana shi ne Granit Xhaka, wanda aka dauko daga Borussia Monchengladbach kan kudi fan miliyan 34.
A wasan da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 3-4, sai sauya Aaron Ramsey da Alex Iwobi aka yi a karawar sakamakon rauni da suka yi. Tun kafin a fara kakar wasannin bana Per Mertesacker da Gabriel da kuma Jack Wilshere suna jinyar rauni tare da Danny Welbeck.
Wenger ya ce a shirye yake ya sayo dan kwallo ko nawa ne kudinsa, matsalar ita ce ba za ka samu irin dan wasan da kake bukata ba.
Asali: Legit.ng