Kocin Arsenal ya kara caccakar kasuwar sayen yan wasa. Kocin Arsenal ya kara caccakar kasuwar sayen yan wasa.
–An caccaki kocin Arsenal kan yadda tsarin kasuwancin shi yake.
–Ba da dadewa ba Wenger ya caccaki manyan kungiyoyi kan yadda suke sayen yan wasa .
–Mai horarwar ya kara kare kanshi.
Mai horarwar da Arsenal Arsene Wenger ya caccaki kasuwar sayen yan wasa, kan korafin da ake mashi a kan ya fidda kudi yayi sayayya. An caccaki kungiyar Arsenal kan yadda suke kasuwancin yan wasa na kakar bana , inda wenger ya saya Granit Xhaka da Takumo Asano da Rob Holding da da yawan masu raunuka da yan wasar kungiyar suke fuskanta.
Kocin yak are kanshi inda yace yace yana da alhaki kan baya so yayi sayayya kara zube’’dan me kuke cewa bana son kasha kudi,ban fahimci hakan ba ,in na saya dan wasa na £45, nayi da kyau kenan,in na saurare ku, amma kasha kudi shi kanshi bba ta hanyar da ta dace ba,ba abu mai amfani bane.
Wenger ya bayyana cewa’’zan iya kasha kasha miliyan £300 gurin sayen yan wasa-in ina da su. Mu kungiya ce masu ma’aikata 600 wadanda suke da nauyin da yake rataye a wuyansu. In muka samu yan wasa wadanda zasu taimake mu, baza mu ji kyashin sayen sub a.
Ya kankare bayaninsa da cewa’’magoya bayanmu suna da kyakykyawar alaka da kafofin yada labaari,muna kokarin yin abin da ya dace abin mai sauki ne, mahukuntar kungiyar suna kokarin aiki tukuru dai-daita kungiyar.
Asali: Legit.ng