Abubuwa hudu da Mahajjata zasu yi
Musulmai yan Najeriya masu niyyar zuwa Hajji sun fara tafiya zuwa kasa mai tsarki don gudanar da Hajji.
Hajji babban lamari ne a Musulunci, haka yasa ya zamto daya daga cikin ginshikan addinin. Sa’annan yin aikin Hajji nauyi ne da Allah ya daura ma masu arziki kacal. Watannin da ake fara gudanar da aikin Hajji sune Zul-qida da Zul-haj.
Musulmai dake hajji sukan gudanar da ibadu iri iri da zaran sun isa garin Makkah da Madina, amma akwai muhimman ibadu guda hudu da zuka wajabta akan kowani Alhaji ko Hajiya.
1.Ihraam
Ihraam na nufin rufe dukkan jiki ta hanyar daura farin zani, dole ne mahajjata su daura farin zanin nan don rufe jikinsu.
A Mikati ake sanya, sa’annan kowane kasa nada irin nata Mikatin, Mikatin kasar Najeriya daban yake da na sauran kasashe. Wajen sanya Ihraami, ana bukatan maza da suyi amfani da falle biyu, su kuma mata suyi amfani da falle uku. Namiji zai daura falle daya kamar zani, dayan fallen kuma a kafadarsa, sai ya fito ta hammatarsa.
Ba’a son mutum yayi zagi ko cin mutuncin wani idan har yana cikin ihraami, kuma an haramta masa farauta don cin nama. Allah SWT yayi bayani cikin surah ta 2 aya na 197 na Al-Qur’ani dangane da watan Hajj da kuma abin da ake bukatan mahajjati ya kaurace ma: “ana yin Hajji a watanni sanannu; don haka Hajj ya wajaba akansa, ya sanya Ihraami, ba’a yarda ya sadu da iyalinsa ba, rashin da’a da kuma fada a yayin Hajji. Duk alherin da kayi, Allah na sane da shi. Sa’annan kayi guzuri, amma mafi alherin guzuri shine tsoron Allah, ku ji Tsorona (Allah), mutanen dake da fahimta”
2. tsayuwan Arfa
Wannan shine mafi muhimmancin ibadun da akeyi yayin gudanar da aikin Hajji. Duk wanda ya rasa tsayuwar Arfa toh kamar yayi asarar Hajjinsa ne, dalili kuwa shine, Manzon Allah SAW yace Arfa shine Hajji.
Musulmai suna tsayuwa ne a dutsen Arfa a ranar 9 na watan Zul-Hajj, zasu saurari huduba daga liman. Daga nan sais u gudanar da sallar Azahar da La’asar kafin su wuce Muzdalifa da yamma. Arafa shine sunan dutsen ke tsayuwa a ranar.
3.Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa
Safa da Marwa wasu duwatsu ne dake garin Makkah, ana bukatan mahajjata suyi sassarfa daga Safa zuwa Marwa, Marwa zuwa Safa, har yayi haka sau bakwai. Allah ya ambaci guraren biyu a cikin Alqur’ani, sura ta 2 aya ta 158.
4. Dawafi
Dawafi na nufin zagayen dakin Ka’aba sau bakwai wanda ake faraway daga dutsen Hajarul Aswad.
Ana bukatan da zarar Mahajjaci ya isa garin Makkah da ya yi dawafi. Bayan an fara Hajji ma ana son mahajjaci ya kara yin dawafi, haka zalika mahajjaci zai yi dawafi idan ya kammala Hajji, wannan shine kamar dawafin bankwana.
Amma fa mahajjaci zai iya yin dawafi a duk lokacin da ya gadama, ba’a kiyasta iyakan lokacin da mutum zai yi dawafi ba.
Asali: Legit.ng