Al’adun aure masu ban mamaki na wasu kasashe
Ga wasu al’adu da ake yi a wasu kasashe yayin bikin aure masu ban mamaki da kuma ban haushi.
Mayar da baki ya koma fari
A al’adar yankin Scotland na kasar Britaniya ango da amarya ake yiwa wanka da tarkacen ragowar abincin har sai koma bakake.
Rawa da Amarya ko Ango sai an biya
A kasar Poland a shagalin biki, amarya da ango ba sa rawa da kowa sai wanda ya biya, kudin da aka tara kuwa, ba na mawaki ba ne, na ma’auratan ne, su je su huce gajiya.
Auren Dabba
A kasar India sun yarda da auren dabba domin korar bakin aljani musamman idan mace mummuna ce, a bisa al’adarsu sai ta auri kare ko biri ko akuya domin korar aljanin da ke tare da ita. Sai dai, amaryar ba ta tarawa da dabbar.
Satar amarya
A kasar Kyrgystan idan kana son mace sai ka sace ta ka kai gida wajen iyayenka, ba za su sake ta ba har sai ta yarda za ta aureka.
Daukar Amarya a kafada
Al’adar gargajiya ta Turai, Ango saba amayar ya ke yi a kafadarsa daga inda aka daura aure har kofar gidansa.
Bude kofa
A kasar Malawi wani kato a ke samu ya kwana da wacce za a aurar da sunan bude kofa. Iyayenta kuma su biya.
Tofi a kan amarya
A kabilar Masai a Kenya, amarya aske mata kai ake yi, sannan a shafe mata shi da kitsen tunkiya, mahaifinta kuma ya tofe kan da kuma kirjinta da yawu don samu albarka.
Asali: Legit.ng