Hatsarin mota ya lakume ma’aikatan lafiya hudu a hanyar Kano

Hatsarin mota ya lakume ma’aikatan lafiya hudu a hanyar Kano

Ma’aikatan lafiya na asibitin Murtala dake jihar Kano su hudu ne suka rasa rayukansu a wani mummunar hatsari daya afku kan babban hanyar Zari zuwa Kano da safiyar ranar Laraba, 17 ga watan agusta.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, ma’aikatan na kan hanyarsu ta yin ta’aziyya ga wani abokin aikin su da yayi rashin dan uwansa. Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a Jaji, bayan motarsu ta fadawa wata babbar mota.

Hatsarin mota ya lakume ma’aikatan lafiya hudu a hanyar Kano

Shugaban sashin magani na asibitin ya bayyana sunayen mamatan kamar haka; Abdulhamid Abudulkadir, Salisu Mohammed, MaiLadan da kuma wata karamar ma’aikaciya mai suna Marry. An yi jana’izar su kamar yadda musulunci ya tanadar, ita kuma Marry yar asalin jihar Adamawa an mika tag a danginta.

Duk kokarin da majiyar mu tayi don jin tab akin hukumar kare haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kaduna yaci tura har zuwa lokacin hada wannan labarin.

Kazalika an samu wani mummunar hatsari da ya lakume mutane 12 a hanyar Bauchi zuwa Kano, majiyar gani da ido sun bayyana cewa mutane 11 daga cikinsu ma’aikatan tsaro ne da wani kamfani mai suna Danga Security, kuma suna kan hanyar dawowa ne daga Ningi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng