An gano gidan Fursuna da mahauka sama da 80

An gano gidan Fursuna da mahauka sama da 80

-Gidan yarin Umuahia na tsare da mahaukata 80

-Ana tsare da kimanin mutane 374 yayin da 116 na jira a yanke musu hukunci

An gano cewa ana tsare da marasa hankali sama da 80 a gidan yari na Umuahia wanda ke karkashin kulawar gwamnatin yarayya.

An gano gidan Fursuna da mahauka sama da 80

Hakan ya fito fili ne a yayin da mataimakin sufiritanda na hukumar kula da gidajen yari na tarayya DSP Kalu Ikpe ya magantu kan al’amarin a cewar jaridar Vanguard.

DSP Ikpe ya bayyana cewa, Hukumar na iya bakin kokarinta na kula da masu tabin hankalin da ganin cewa sun samu lafiyar da za su iya fuskantar shari’oin da a ake yi musu a jihar, sannan ya kuma kara da cewa, A nan umuahia babu gidan mahaukata, haka mu ke karbar daurarru, sai dai idan mun lura da suna da tabin hakali, mu kan aika da su Aba a inda ake da asibitin masu tabin hankali”.

Mista Ikpe ya kuma kara da cewa, ba sa watsi da wadanda ke cikin larurar tabin hankali, domin duk wanda suka ga da alamun tabuwa suna tura shi wajen Likitan masu tabin hankali, wanda ya ke aiki da su a kullum.

Sai dai ya bayyana cewa hukumarsa ba ta yadda za ta gano cewa wanda aka daure yana da tabin hankali ko babu a lokacin da kawo musu shi, in ban da takardar ummarni kame mutum watau waranti na  hukuma, amma idan ya gagaresu sai sukan sanar da kotu halin da wanda aka daure ya ke ciki, domin daukar matakin da ya fi dacewa.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng