Hakikanin Ma’anar kalmar Jihadi

Hakikanin Ma’anar kalmar Jihadi

Yawancin mutane ga fassara Kalmar Jihadi da daukar makami da kisa, da sunan musulunci. A hudubar Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya bayyana ainihin ma’anar Kalmar da kuma abin da ta ke nufi, ga kadan daga ciki

Hakikanin Ma’anar kalmar Jihadi
Musulmai bayan sallar Juma'a

Ma’anar Kalmar jihadi ita ce kokari domin Allah a kan tafarki madaidaici, wannan kokari na daukar siffofi daban-daban, kamar na zuci, wajen samun tsarkakkakkiyar zuciya da kubuta daga sabawa Allah, da kokari na gujewa sabonsa, da kuma  ta bayyane, watau kokari ta hanyar wajen taimakon mabukata, da kuma al’umma ta yadda za ta samu zaman lafiya, hadin kai da ci gaba.

A inda aka ambaci Jihadi a da daukar makami, shi ne wajen kare al’umma daga yaki na makamai. Jihadi bai taba zama Al-harb al-mugaddis yaki da makami mai tsarki ba, saboda a musulunci babu wani abu wai shi yaki mai tsarki kamar yadda ake cewa ‘holy war’, yaki na iya zama kan adalci ne ko na zalunci.

Dalilin yaki a musulunci shi ne a kare masu rauni, da kuma wadanda ba su ji ba, ba kuma su gani ba, daga zalunci, da kuma ba kowa dama na ya yi addininsa ba tare da tursasawa ba.

Al kur’ani da Sunna, da kuma haduwar manyan malaman musulunci, tun farkon bayyanar addinin har zuwa yau, ya bayar da damar daukan makami ne kawai domin mayar da martani ga zalunci da kuma danniya, manyan malamai na musulunci sun yi littafai masu yawa a kan yaki da zuciya, wanda shi ne babban yaki amma ba na makami ba, kamar yadda ya zo a hadisan Manzo Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel