Gwamnan Kano ya kafa tarihi a Arewa

Gwamnan Kano ya kafa tarihi a Arewa

-Gwamnan ya kafa tarihi da nadin mace a matsayin babban akantar jiha da kuma arewa

-Wacce aka nada tsohuwar ma’aikaciyar kuma kwamishiniyar kula da kasafin kudi da tsare-tsarare

-Maihafinta tsohon akanta ne a jiha

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa tarihi a jihar Kano da kuma arewacin Najeriya da nadin mace ta farko a matsayin a Babbar Akantar ta jihar.

Gwamnan Kano ya kafa tarihi a Arewa
Babbar Akanta ta jihar Kano, Mace ta farko a tarihin kafuwar jihar Kano a shekaru 49

Wacce gwamnan ya nada ita ce Hajiya Aishatu Muhammad Bello kwamishiniyar kula da kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar.

An haifi Hajiya Aisha a unguwar Kofar Mata a cikin birnin Kano, ta kuma yi karatunta a makarantar firamare ta K/Nassarawa da kuma makarantar mata ta Shekara, ta kuma yi karatunta na sakandare a GGC Dala, kafin ta halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, a inda ta yi digiri a fannin kula da ma’aikata da kuma fannin kudade, ta kuma yi digirinta na biyu a fannin hulda tsakanin kasa da kasa.

Aisha ta rike matsayi daban daban a aikin banki, ciki har da Manaja a Habib Bank, da Keystone Bank, da kuma First Bank, kafin a nadata a mukamin Kwamishiniya mai kula da kasafin kudi da kuma tsare-tsare ta jihar.

Hajia Aisha, za a iya cewa ta gaji mahaifinta Alhaji Sani Abubakar Liman ne, wanda ya taba zama Akanta a Hukumar kula da otal-otal da kuma Kamfanin sayar da kayyakin gona na KASCO duk a jihar Kano, da kuma babban mai binciken kudi na Hukumar kula da birnin tarayya Abuja FCDA, Hajiya Aisha na auren Alhaji Muhammadu Bello Magajin garin Raba na Nupe, ta na da 'ya 'ya da kuma jika.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel