Mutumin da yafi yawan yaya a Duniya ya kafa tarihi

Mutumin da yafi yawan yaya a Duniya ya kafa tarihi

A yayin da wasu matan ke gudun sake haihuwa saboda wahalar dake tattare da hakan, wata kuma ke kaunar cigaba da hayayyafa.

Sama da shekaru 300 da suka gabata tsakanin shekarun 1725 da 1765 aka samu wata mata da ta auri wani manomi dan kasar Rasha mai suna Feodor Vassilyev inda ta haifa masa yaya 69. Ita dai matar ta samu daukan ciki sau 27.

Mutumin da yafi yawan yaya a Duniya ya kafa tarihi

Feodor tare da matarsa da yayansa

A cewar kundin tarihin duniya, matar ta haifi tagwaye yan biyu sau 16, yan uku sau 7, sai kuma yan hudu sau 4. Duk da cewa tagwaye daya sun rasu tun suna jarirai, sauran yaya 67 sun rayu. A shekarar 1782 ne aka sanar da labarin wannan mata a dakin masu bautan gargajiya na Nikolsk dake rubuta bahasin duk haihuwar da matar tayi.

Abin mamakin shine, Feodor ya kara aure bayan rasuwar matarsa ta fari, uwar yayansa 69. Matar ta biyu ta dauki ciki sau 8, inda ta haifa masa yaya tagwaye 6, da yan uku guda 2, gaba daya yaya 18.

A lokacin da Feodor ya kai shekaru 75, 82 daga cikin yayansa na nan da ransu da lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng