Dan wasan Manchester United yayi hasashen yadda kungiyar zata kasance a karkashin Mourinho.
_ Manchester sun siya manyan yan wasa a wannan siyayyan yan was an da akeyi.
_ Parker ya bukaci Mourinho daya kara sayen yan wasa.
_ Dan was an dai yayi bayani akan yadda Manchester zata kasance.
Acewar dan was an Manchester United Paul Parker, yace Manchester suyi hankali domin suga sun fada cikin jerin kungiyoyi na hudu a teburi. Ibrahimovic. Har ilayau kuma, Parker, wanda yaci kofuna biyu a kungiyar ta United, ya tabbatar da sai kungiyar ta kara gyaran yan wasanta. Dan wasan ya tabbatar da dacewa Mourinho saiya sake sayen dan wasan tsakiya guda daya dakuma dan wasan gaba shima guda daya.
Parker yace, “ Har ilayau, Manchester United basu gama siyayya ba, saboda saisun kara siyan dan wasan tsakiya guda daya, sannan kuma su sayi dan wasan gaba guda daya. Saboda yan wasan da kungiyar take dasu yanzu bazasu iya chima kungiyar kofiba, saboda haka yazama dole Mourinho ya sake komawa kasuwa idan dai har yanason yaci kofi.
Yakuma kara dacewa; Zaku iyacewa Manchester zata iya karewa na hudu idan mukayi la’akari da wasan da suka buga da Bournemouth? Zan iya cewa gaskiya da kyar ne?
Tsohon dan wasan ya kara dacewa “ Liverpool suna da kyau sosai, amman kungiyar Arsenal dole sai sunyi gyara. Tottenham da Chelsea zaiyi wuya a fasasu, dan haka sudai sunanan. Saboda haka United yakamata suyi wani abu daganan zuwa karshen watan Agusta, su kawo akalla yan wasa guda uku domin su samu damar zuwa gasar chin kofin chamfiyon lig koma su dauki kofin.
Asali: Legit.ng