Rundunar sojan ruwa tayi bajakolin jiragen yaki 30 kirar Najeriya
A ranar larabar data gabata ne rundunar sojan ruwa tayi bajakolin wasu jiragen yaki guda 30 wadanda aka kera a Najeriya da zasu taimaka wajen yaki da yan ta’adda da masu aikata manyan laifuka.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta ruwaito, rundunar sojan ruwaan ta kaddamar da jiragen ne guda 39, 30 daga cikinsu a Najeriya aka kera su, kazalika rundunar sojan ta kaddamar da motocin sintiri huda 45.
A yayin bikin kaddamarwar, ministan tsaro, Mannir Dan Ali, yace an sanya ma jiragen yakin makaman kare dangi da kuma ingantaccen kariya don samar da ingantaccen tsaro. Ministan ya samu wakilicin babban sakataren ma’aikatan tsaro Mista Danjuma Sheni yace “kalubalen tsaro da ake fama da shi a Najeriya na bukatan kudi da kayan aiki don kawar da ita, amma a wannan marran da ake ciki na karancin kudi yasa dole mu dage wajen magance matsalar”.
Dan Ali yace jiragen da tsawon su ya kai mita 8.2, an gina su ne a farfajiyar yadin rundunar soja ta Epenal dake Fatakwal za’ayi amfani dasu ne wajen sintiri a yankin Neja Delta, inda kuma sauran motoci 20 na zuwa nan bada dadewa.
“ina fatan jiragen da aka kaddamar yau zasu taimaka wajen sintirin da ake gudanarwa a tekuna daban daban na kasar nan, don ya amfanar da bangaren ruwan kasar nan” inji shi. Sa’annan yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari godiya don irin gudunmuwar da yake baiwa kokarin rundunar soja. “ba makawa wadannan jiragen zasu taimaka ma aikin soja, cikin yunkurin da muke yi shine mu magance duk wani matsalar tsrao a kasa, da haka ne muka kaddamar da jiragen ruwa 39 cikin wata shida.
“kokarin da mukeyi, a baya da kuma yanzu na nuni da gudunmuwar da rundunar sojan ruwa ke bayarwa wajen tsaron kasa. “9 daga cikin jirage 39 an siye su ne daga Sri Lanka, kuma zasu taimaka wajen sintiri akan ruwan Najeriya” inji shugaban rundunar Ete Ibe. Ya kara da cewa rundunar sojn ruwa ta kera jiragen ruwa na yaki guda 60 cikin nasu kokarin wajen samar m rundunar tasu kayan aiki.
“kalubalen kudi tare da matsalar tsaro da ake fama das hi a yanzu yasa dole rundunar sojan ruwa ta nemi hanyar tsuke lalitar ta hanyar kera wadannan jiragen da kansu. “kudin da aka kashe wajen kera wadannan jiragen bai kai rabin kudin da za’a kashe ba wajen siyansu daga kasashen waje. “wadannan jiragen na dauke da kayayyakin yaki da makamai daban daban.” inji Ete Ibas.
A cewar shugaban rundunar sojan ruwan Ete Ibas, jiragen suna da kariya ingantacce don samun tsaro. “muna sa ran zasu taimaka wajen samar da muhimmin tsaro da kuma kawo gyara. “zan iya cewa mun kusa mamaye gaba daya ruwan Najeriya da jiragen ruwanmu don samar da tsaro mai kyau.”
Ete ya kara da cewa za’a mika jiragen bangarorin da suka dace na rundunar sojan ruwa. Shugaban kwamitin sojan ruwa na majalisar dattijai yace kamitin sa na iya kokarinta wajen ganin tayi duk mai yiwuwa wajen magance matsalar tsaro akan ruwan Najeriya.
Daga cikin wadanda suka samu halattan bikin akwai shugaban hafsan soja, janar Gabriel Olanisakin da sauran manyan sojojin kasar nan.
Asali: Legit.ng