An baiwa Bolori da Aisha wakil beli
–Rundunar sojin najeriya sunce suna neman wasu mutane 3 ruwa a jallo saboda alakar su da Boko haram
–Hukumar sojin najeriya sun baiwa Ahmed bolori da Aisha Wakil beli
Rundunar sojin Najeriya ta bauwa Ahmed bolori da Aisha Wakil beli bayan sun ce suna neman su ruwa a jallo. An basu belin ne bayan sun cika wasu ka'idoji,harda bada fasfot din tafiyarsu.
Wani babban hafsan soja wanda aka sakaya sunansa ya bayyana cewa har yanzu ana gudanar da bincike yayinda ake jiran zuwan na ukun ,Ahmad salkida wanda ke zaune a kasar Dubai, wanda kuma akafi sani da muryan Boko Haram.
An alanta neman mutane ukun ruwa a jallo ne bayan sabuwan bidiyon da yan kungiyar boko haram suka saki mai kunshe da yan matan chibok. Kafin Hukumar sojin najeriya ta saki jawabin dalilin da yasa ake neman su , hedkwatan tsaro sin saki jawabin cewa sun samu alaka sakanin mutane 3 nan da boko haram.
KU KARANTA : Boko haram sun kashe mutane 5 a hanya
Jawabin da suka saki na da take , Rundunar sojin najeriya suna alanta neman. Ahmed Salkida (Ambassador), Ahmed U Bolori da Aisha Wakil ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng