Shugaban Fulani ya mika makamansa ga sojoji a Zamfara

Shugaban Fulani ya mika makamansa ga sojoji a Zamfara

-Wani shugaban Fulatan ya mika makamansa da kuma  alabarusai

-Barnar da Fulani makiyaya suke yi da makamai ya ja baya

-Kakakin rundunar sojin kasar ne ya yi cikakkken bayani

Shugaban Fulani ya mika makamansa ga sojoji a Zamfara

Wani shugaban Fulani makiyaya a jihar Zamfara ya mai suna Alhaji Ruwa, a bisa ra’ayin kansa, ya mika makamansa da kuma wasu albarusai ga rundunar soji ta bataliya 223 da ke karkashin Briged ta 1 da ke jihar Zamfara.

Alhaji Ruwa ya mikawa sojojin wasu bindigogi biyu kirar gida, da kuma bindigogin farauta guda uku ga sojin, ya  kuma yi alkawarin shawo kan mutanensa da suma su ajiye na su makaman ba tare da bata lokaci ba.

Kakaki, kuma mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na rundunar sojin kasa, Kanar Sani Kuka Sheka Usman ne ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, Alhaji Ruwa ya dau alkawarin shawo kan sauran makiyaya da ke dauke da makamai da su fito da su mika makamansu ga gwamnati.

Shugaban Fulani ya mika makamansa ga sojoji a Zamfara
Yaran Fulani Makiyaya da shanunsu

Wannan a cewar Kuka sheka, “ na daya daga cikin nasarorin da ake samu na raba jihar Zamfara da satar shanu da kuma ta’addancin ‘yan bindiga  a yanki.”

KU KARANTA: Ana daf da kai mana hari – Basaraken Abia

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Ekiti ta amince ta ware filin kiwo ga Fulani makiyaya a jihar, an cimma wannan matsaya ne bayan da aka dade ana tattaunawa tsakanin Fulanin da kuma gwamnatin.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel