Ambaliya mai karfi ta hako gawarwaki a makabartun dake US.
- Bayan kwanaki da ruwan sama mai karfi, ambaliya ta hako gawarwaki da akwatunan gawa a makabartar dake Louisiana dake USA.
- A kalla mutane bakwai sun mutu kuma an ceto sama da 20,000 daga yankunan da abun ya shafa a jahar.
- Gwamnan Louisiana yace, ambaliyar ya kafa wata tarihi a jihar kuma wata kilama tafi guguwar katrina barna.
Akwatinan gawarwaki na yawo cikin ruwa a makabartar dake Louisiana, Ambaliya a jahohin gamayya a kasar Amerika ya tayar da hayaniya a kasar bayan da akaga ya tono gawarwaki daga makabarta. Rahoto daga Metrouk sunce bayanar gawarwakin daga makabartun a Louisiana ya farune saboda yawan ruwan da akayi a yankin.
Wata mai suna Anna johnson,ta dauki hotuna da akwatunan gawarwaki a makabartan inda tace lallai ambaliyar mai karfi ne. Tace "Bamu taba ganin irin haka ba. Yafi guguwar Katrina bala'i, yanzu haka mijina na cikin masu bada ceto. Yanada kwale-kwale dan haka yake taimakawa wa'anda hakkin ceto ya wajabta a kansu".
Asali: Legit.ng