Mai sayar da mushen kaji ga jama’a ya shiga hannu a Kano

Mai sayar da mushen kaji ga jama’a ya shiga hannu a Kano

Wani wanda ake zargi da sayar da mushen kajin gidan gona ga jama’a ya shiga hannu a jihar Kano.

Dubun matashin wanda ya bayyana da Sama’ila ya cika ne a yayin da ya fada hannun ‘yan sintirin kungiyar Vigilante ta unguwar ‘Yar Akwa da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.

Mai sayar da mushen kaji ga jama’a ya shiga hannu a Kano
Tsiren dakwalen kaji a gaba wuta

A wani rahoto da wani gidan Rediyon jihar ya bayar cikin shirinsa na Mu karkade kunnuwa, a inda aka yi hira da matashin da kuma mushen kajin guda 10 a hannunsa, ya ce, yau ce ta sa shi yin hakan.

KU KARANTA: Wata ta sayar da dan cikinta kafin ta haife shi

Matashin ya ce, ya na samun matatun kajin ne daga wani gidan gona a idan ake zubar da su, sai ya diba ya kuma gyara, sannan ya sayarwa wandanda a cewarsa ba musulmai ba ne, a inda su kuma su ke suke tafiya da su garuruwansu.

Sai dai Isiyaku Garba Kwamdan ‘yan kungiyar Vigilante da ke sintirin ya ce, karo na uku ke nan Sama’ila yana fadawa tarkon su, a inda matashin ya yi musu alkawarin ya tuba ba zai sake ba, sai ga shi ya sake shiga hannunsu, don haka wannan karon ba za su kyale shi ba, yana mai cewa,

“… Ko ba Musulmi ne za su ci wannan naman ba, da akwai hadari. Ballantana ba bu tabbacin cewa  kabilun da muke tare da su, da kuma wasu bata gari, ba mushen kajin suke saye suke sa wa a abincin sayarwar da muke ci ba, don haka a wannan karon za su mika shi ne DPO na yankin.”

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel