Dalilai 5 da ke sa haihuwar tagwaye
Mutane da yawa dai suna matukar sha'awar yan biyu. So dayawa kuma akan yi ta yiwa ma'aurata murna idan har suka same su.
Ma'aurata ma dai da yawa suna matukar kaunar yan biyu a lokuta da dama.
Akwai yan biyu ma kala-kala kuma wasu na kama da juna sosai yayin da wasu kuma basa kama. Wasu na zuwa jinsi daya yayin da wasu kuma ke zuwa jinsi daban-daban. Akan canfa su a wasu lokuttan ace wai sunayin wani abu da ake kira a kasar hausa wai shi "kwafi" musamman ma idan aka bata musu rai.
A nan kasa kadan zamu kawo wa mai karatu wasu halaye ko dabi'u dakan sa ma'aurata su haifi tagwaye.
(1) Idan ka/kin gada
Ko shakka babu ana gadar haihuwar tagwaye kamar yadda wannan wani sanannen abu ne a rayuwar mu ta yau da kullum. Mutanen da suka fito daga gidan da ake da yan biyu a lokuta da dama sukan haifi yan biyu su ma.
(2) Shan magunguna
Yanzu haka dai ci gaban kimiyya ya karu inda akwai wasu magunguna da ake bayarwa a asibiti da suke taimakawa ma'aurata wajen haihuwar tagwaye. Kawai ma'aurata masu sha'awa sai su garzaya wajen likitan su yayi musu bayani.
(3) Yanayin abinci
Sanin kowa ne cewar abinci yana da matukar muhimmacin a wurin tafiyar da rayuwar dan adam. Bincike yanuna cewar mata dake cin abinci mai madara-madara koma madarar kanta suna da yiwuwar samun tagwaye fiye da wadanda basu ci.
Akwai wata nau'in doya ma da ke akwai a kasar yarbawa wadda akayi imanin cewa tana sa haihuwar tagwayen.
(4) Kabila
Ita kabila tana da matukar anfani a wajen haihuwar tagwaye. Wata kabilar an santa sosai wajen haihuwar an biyu fiye da wata.
(5) Shekaru da kuma girman jiki
Bincike ya nuna cewar manyan mata sun fi haihuwar yan biyu fiye da yara kuma marasa kiba. An dai gano cewar matan da suka haura shekaru 30 sun fi haihuwar tagwaye.
Asali: Legit.ng