Sai mun ladabtar da Jibril - Majalisa

Sai mun ladabtar da Jibril - Majalisa

Bulaliyar majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa yace majalisa zata ladabtar da tsohon shugaban kwamitin kasafi na majalisar Abdulmuminu Jibril saboda yadda ya janyo ma majalisar abin kunya.

 

Sai mun ladabtar da Jibril - Majalisa

 

Doguwa yace zargin da Abdulmuminu keyi na aringizon kasafin kudi ba gaskiya bane, yayi haka ne kawai don ya ci mutuncin majalisar, da kuma ramuwar gayya don cire shi a kujerarsa da aka yi. Jaridar Punch ta ruwaito shi yana cewa:

“shi (Jibril) ya ruga gaban kotu ne kawai don tana tsoron irin horon da za’a mai. Wannan wata dabara ce ta Jibril don kare kansa daga fushin majalisa a dalilin zargi mara makama da yayi ma majalisar don cin mutuncinta. “sa’annan yayi nasarar janyo majalisa abin kunya, wadda hakan laifi ne a karkashin sashi na 24 da 33 na dokokin majalisa. don haka dole ne irin wannan keta haddin majalisar ba zai wuce ba sai an ladabtar da mai laifin.

“ya kamata yan Najeriya su sani cewa karairayi kawai Jibril ke yi musu. Da yake a yanzu ya gane cewa ruwa ya kare ma dan kada, shi yasa ya ruga gaban kotu, kuma ina da yakinin ba zai samu nasara ba a can.”

Bulaliyar majalisar yayi barazanar gurfanar da Jibril da kansa bayan majalisa ta dauki mataki a kansa. Amma fa Jibril ya bada wani sanarwa, inda ya kara fidda wasu sabbin zarge zarge akan kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, yana cewa Kaakakin ya fidda wasu makudan kudade don biyan yan majalisar don su yake shi.

“ina da labarin wani abokin Dogara dake shugabantar wata sananniyar hukumar gwamnatin tarayya yana bin yan majalisa da tayin basu kudi don su goyi bayan Kaakakin.” Inji Jibril. ya kara da cewa a yanzu haka ya aika wasika zuwa ga kwamitin da shugaban kasa ya kafa mai bashi shawara akan yaki da cin hanci da rashawa a ranar Litinin, inda ya nemi da su bashi dama ya gurfana a gabansu don ya zube musu bayani dangane da zarge zargen da yayi ma kaakakin majalisa Dogara.

Jibril yace “na fara yin ma jakadun kasashen waje dake kasarnan bayani, kuma nan da kwanaki kadan zan mika bayanai na ga ofishin jakadancin kasashen Birtaniya, Amurka, Faransa da kuma Jamani dake Najeriya. “irin zantuttukan da Dogara yayi a yan kwanakin nan, kamar yadda yace wai aringizo ba laif bane, ya nuna gaskiyar zargin da nayi masa. “don haka na mika ma hukumar karbar korafi na kasa da hukumar kare hakkin bil adama takardan koke don su kare da kuma tabbatar min da hakkokina.”

Idan ba’a manata ba, Abdulmuminu Jibril yace yayi nadamar rawar da ya taka wajen ganin Yakubu Dogara ya zama Kaakakin majalisar wakilai. Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aika ma shugaban jam’iyar APC John Oyegun. Yace ya rubuta wasikar ne saboda wasu kwararan hujjoji guda hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng