Ikon Allah! Ga garin da yafi ko ina 'yan biyu a duniya

Ikon Allah! Ga garin da yafi ko ina 'yan biyu a duniya

A baya dai wasu kabilu a kasar nan sun canfa yan biyu ina a wurare da dama ake kashe su idan an haife su amma yanzu sai gashi an samu wani gar a cikin kasar da ya fi ko ina a cikin duniyar nan yawan 'yan biyu.

Ikon Allah! Ga garin da yafi ko ina 'yan biyu a duniya

Garin wanda yake a wajen garin Legas ana ma yi masa lakani ne da "garin yan biyu" kokuma "babban birnin tagwaye". Ana dai cewa garin Igbo-Ora.

Garin dai yana da kimanin mutane 60,000 kuma an yi hasashen cewar akwai wata doyar da matan garin suke ci da take da alaka da yawan haihuwar 'yan biyun da suke yi. An dai ce doyar tana kara masu karsashi ne da kuma damar samun yaya biyu.

Su kuwa yan garin sun yi amannar cewar su wasu mutane ne na daban kuma na musamman da Allah ya halitta kuma ya azurtasu da abinci mai kyau mai kuma kara masu karsashi.

Wakilin mu ya bayyana mana cewa a mafi yawancin mutanen garin akan samu akalla yan biyu ko da sau daya ne a kowanne gidan a garin. A garin Igbo-Ora, kusan ko ina ka waiga zaka ga yan biyu suna yawa ko wasa, maza da mata kuma yara da manya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng