Zafin kishi: Mace Mai ciki ta kone kanta
Kishi kumallon mata amma abin da wata mata mai ciki ta aikata, in ji masu iya magana, ya wuce min sharri, ya kai matuka a tsananin kishi, a cewar masu lura da al’amura.
Wata mai dauke da tsohon ciki, Cynthia Njoki a kasar Kenya ta cinnawa kanta wuta ne a bisa zargin bin mata da ta ke yiwa mijinta.
Rahotan da aka nuna a wani gidan Talbijin a kasar Kenya KTN, na cewa mai ciki Cynthia, ta dau wannan mataki ne bayan da maigidanta ya kasa bayyana mata inda ya kwana a ranar Lahadin 13 ga watan Agusta a wata unguwar marasa galihu da ake kira Langa-langa a kasar.
A hirar da aka yi da mahaifiyar mai cikin da ta yi wannan danyen aiki Mary Wangui, Cynthia ta ce yi ta kiran wayar mijin ne a inda wata ta dauka ta kuma ce suna tare a lokacin, jin hakan ya sa ta ta garazaya ta samo kanazir ta zuba a jiknta ta kuma kyasta ashana.
ta ma’aikaciyar asibitin da aka kai matar, Jenefer Methenge, a yi hirar da aka yi a rahoton, ta ce an kawo Cynthian ranga-ranga ne a asibitin a inda kuma suka yi abin da ya kamata su yi mata na magani, domin kunar ta kai kashi 45 a jikinta, sai dai ba a sani ba ko jarrin da ta ke dauke da dan wata 6 zai rayu.
Mijin matar mai sana ar kanikanci wanda kuma ba a bayyana sunansa ba, yaki ya ce komai saboda kaduwa dangane faruwar lamarin a cewar rahoton.
Asali: Legit.ng