Buratai yace horo nada muhimmanci a aikin Soja

Buratai yace horo nada muhimmanci a aikin Soja

–Buratai yace bazasu yarda da rashin kuzari ba

–Shugaban rundunar sojin Najeriya yace aikin horo ne da kuma tarbiyya nada muhimmanci a rayuwar soja.

–COAS  ya rantsar da dalibai 200 zuwa aikin soja

Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Lt. Janar Tukur Buratai ya yi jawabin karama hafsosin soji karfin guiwa . ya Kira da su cewan su dinga motsa jiki domin koshin lafiya. Yace baza'a yarda da rashin kuzari a gidan soja.

Buratai yace horo nada muhimmanci a aikin Soja
Lt Gen Tukur Buratai

Shugaban rundunar sojin Najeriya ya bayyana haka ne ga wasu dalibai 200 na  Regular Course 63, Wadanda suka kamalla horo a makarantan sojin najeriya NDA da ke Garin Jos,Jihar Flato. Kana, Buratai ya bayyana ma dalibai da suka kare horon cewa su zama abin alfahari ga kasa; saboda haka su kasance cikin farga a kowani lokaci.

“Ina son in fada muku cewa a gidan soja babu gafala. Duk abinda muke yi, muna yin shi ne da tabaci da kuma kuzari. Wani abu mai muhimmanci a gidan soja shine tarbiyya da kuma mots jiki a koda yaushe .

Shugaban rundunar sojin ya jaddada matsalar tsaron da kasa ke ciki , kana yayi Magana akan ta’addancin ke fuskantan arewa maso gabashin kasa . zasu ana kyautata zaton sojin najaeriya zasu kasance a shirye.  “Maganan gaskiya shine a arewa maso gabas, zaku fuskanci farmaki ba tare da Ankara ba musamman bam inda yan kungiyan boko haram suke. Dole ne ku kasance cikin Ankara game irin wannan hare-haren da kuma duk inda aka tura ku daga nan. Kuma bayan ranstar da ku, ina da tabbacin wasu daga cikin ku za’a turasu arewa maso gabas. Domin haka ku shirya zukatanku. Za’a dogara da ku a matsayin jami’an tsaro, dole ne ku kasance masu tarbiyya, babu gafala.

KU KARANTA : FG tayi Magana da boko haram akan sabuwar bidiyon

Hukumar yada labaru a Najeriya (NAN) sun tattaro cewan cikin horon da dalibai suka yi shine : aikin filin daga, shugabanci da kuma irin abinda za’a fuskanta a yankin  arewa maso gabas. Kwanan nan, Shugaban rundunar sojin Najeriya yace ana bukatan hada  karfi da karfe wajen yakan ta’addanci a yankan arewa maso gabashin kasa.

 

 

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng