Muna bukatar karin karfin gwiwa  –Mikel

Muna bukatar karin karfin gwiwa –Mikel

-Kyaftin din kungiyar kwllon kafar Nigeria a Rio ya koka

-Ma’aikatar kula da wasanni ta yi alkawarin ba ‘yan wasan hakkokinsu

-Gwamnati ta yi alkawarin sauke nauyin da ke kanta

Muna bukatar karin karfin gwiwa  –Mikel
Mikel Obi

Kyaftin din ‘yan wasan Najeriya zuwa wasan Olympics da ake yi a Rio ta kasar Barazil, ya yi kira ga Ma’aikatar kula da harkokin matasa da wasanni da cewa suna bukatar kwarin gwiwa.

Wannan kira daga fitattcen dan kwallon ya zo ne bayan da ‘yan wasan suka samu nasara a kan kasar Denmark a karawar da suka yi, a inda suka lallasa ta da ci 2 da 0.

Mikel ne ya ci daya daga cikin kwallaye biyu da suka taimakawa ‘yan wasan kasa da shekara 23 su samu nasara a kan ‘yan Denmark din, sai dai kyaftin din ya ce da akwai bukatar a karfafa musu gwiwa,  ya na mai cewa, “ ….a gaskiya da akwai kalu bale da yawa ,a duk lokacin da muka shiga fili mantawa mu ke yi da komai, mu sa kasarmu a gaba. Za kuma mu ci gaba da yin haka, amma dai muna bukatar a san muna yi.”

KU KARANTA: Rio 2016: Nigeria ta kwabsa a gabannin wasanta da Japan

Bayan da Mista Salvador Chinyeaka ya mayarwa da Mikel kudinsa Dala 4,600 da Mikel din ya biya wa ‘yan wasa kudin otal, gabannin wasan, wakilin Minista Dalong, ya yiwa ‘yan wasan alkawarin cewa gwamnati za ta sauke dukkan nauyin da ke kanta dangane da hakkokinsu. Wakilin Ministan ya kuma jinjinawa ‘yan wasan wadanda duk da matsalolin da suka fuskanta, sun yi ba za ta, sun kuma yi abin da Najeriya ke alfahari da shi.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng