Ana rikici sakanin Hausawa da Igbo a jihar Imo
–Mutane 3 sun rasa rayukansu sanadiyar fada da akeyi tsakanin hausa da igbo a jihar imo.
–Tarzoman ta tashi ne yayinda akace wani bahaushe ya kashe wata mata da yarinya.
–Yan sanda sun ce an kwantar da tarzoman.
Ofishin yan sanda na jihar imo ta ce mutane 3 sun rasa rayukansu sanadiyar wata tarzoma da tayar tsakanin yare a jihar.
Game da NewsAgency of Nigeria, an kashe mata biyu da namiji daya a unguwar akokwa da ke karamar Hukumar ideato a ranar juma'a, 12 ga watan Augusta.
Kakakin yan sanda jihar DSP Andrew Enwerem, ya tabbatar da faruwan ricikin a wata hira da NAN a ranar juma’a a garin owerri, yace wasu sunji raunika. DSP Andrew Enwerem,yace wani mutum dan arewacin najeriya ya je ya kasha watan yarinya da wata mata sa’annan ya kasha kansa. Yace wasu matasa kawai suka tayar da zaune tsaye bayan samun labara. Hakan yasa wasu mutane sun ji raunuka.
DSP Andrew Enwerem,yace hedkwatan yan sandan sun samu labari kuma da wuri kwamishanan yan sanda ya turo yan sanda domin kwantar da rikicin.
KU KARANTA : ‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane a Jihar Ribas
“Wani idon shaida ya fada ma manema labarai cewa yarinyan da aka kasha na talla ne yayinda wani matashi ya bita sai ta gudu wajen wata mata domin neman tsaro. Idon shaidan yace mutmin ya kasha matan da yarinyan.”
Asali: Legit.ng