Adam zango yayi rantsuwa da Alqur'ani akan zargin luwadi
1 - tsawon mintuna
Wannan shahrarren dan fina finan hausa, Adam Zango yayi rantsuwa da Alqur'ani game da zargin aikata luwadi da ake masa. Yayi rantsuwan ne a gidan talabijin din DITV Kaduna.
Adam Zango ya ranste da cewan shi ba dan luwadi bane kuma ba zai zama ba a rayuwan sa.
“Na zo ne domin in fada ma duniya cewan ni ba dan luwadi bane kuma bana tarayya da ayyukan luwadi a kamfanin shirya fina finai da kuma wajen kamfanin.” Ya ce
Asali: Legit.ng