Wani mutum ya kashe kwarton matarshi
-Wani mutum ya aika kwarton lahira ne yayinda ya kama shi a dakin aurensa yana lalata da matarsa
An kama wani mutum mai suna Ezekiel Igbokwe da laifin kasha kwarton matarsa bayan yayi ram dasu suna lalata. Kwarton, Victor Olatundun wanda ya kasance yana sullawa yana lalata da matar mutumin Juliet Igbokwe yana cikin yin lalata ne mutumin ya dawo daga tafiya.
Shi kuma Ezekiel da ya fusata, ya dauki adda ya aika Victor lahira . ma’auratan suna da shekaru 12 da aure da yara 3,duka mazauna Ago-iwoye jihar Ogun.
“Nayi tafiya zuwa Onitsha a ranar 25 ga watan yuli kuma na dawo washe gari ranan 27, nag a wani mutum a cikin daki na sai muka fara dambe. Mutumin yafi karfi na kuma na rasa abinda zany i. sai na dauki adda daga bayan gida na daba masa sara akai. Ya mutu ne a hanyar kaisa asibiti ,abode man feturin motan yan sandan yak are. Ban taba zargin mata na da irin wannan abun ba. Ban yi niyyar kasha shi ba ,aikin shaidan ne , da na san abinda zai faru kenan ,da wuce wa na kawai nayi.”
Nayi niyyan ji masa rauni ne kawai , inje ofishin yan sanda in yi Magana. Ni da mata na bamuyi fad aba kafin tafiya ta Onitsha. Ta haifan mini yara 3. Amma daga baya na san ashe ta taba haihuwa kafin mu hadu.
KU KARANTA : Wata mata ya sanya ma haifaffiyar cikinta guba
Ita kuma Juliet tace :
“Ban san abinda ya sa na bari kwarton ya shigo gidan mijina ba. Idan ni da maigoda na muka samu sabani, zai tafi ya kwashe watanni ya barmr. Nayi wata 6 da sanin olatundun yanzu. Mijina bai kula dani. Zaiyi tafiya ya bar ni da da yara a gidamuna cin wuya.”
Asali: Legit.ng