Na fi karfin EFCC ta bincike ni –Yakubu Dogara

Na fi karfin EFCC ta bincike ni –Yakubu Dogara

-Kakakin majalisar wakilai ya ce Hukumar EFCC ba ta isa ta bincike shi ba

-Wadanda ke kira da a bincike shi jahilai ne

-Babu wani abu wai shi kasafin kudi a tsarin mulki

Na fi karfin EFCC ta bincike ni –Yakubu Dogara
Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara  ya ce, Hukumar EFCC ba ta da ikon bincikarsa a bisa zargin aringizo a kasafin kudin shekara 2016 saboda doka ta ba shi kariya.

Kakakin ya bayyana haka ne wani taro da Cibiyar kula da Manufofi da Tsare-tsaren Shari’a ta shiryawa masu fada a ji a tafiyar da ayyukan jama’a a Abuja, a ranar Alhamis 11 ga watan Agusta, a cewar Premiun Times mai yada labarai a Intanet.

KU KARANTA: Ya kamata EFCC ta kama Dogara –Jibrin Kofa

Rahoton ya ambato Dogara na cewa, wadanda suke kira da a tuhume shi na yin haka ne cikin jahilci, Kakakin sannan ya ce, dokokin da Majalisar tarayya ke aiki da su, sun ba ‘yan majalisa kariya daga tuhuma a yayin da suke gudanar da ayyukansu na majalisa.

Kakakin majalisar ya kuma kara da cewa, “ ….sun manta da sashe na 30 na dokar wanda ke magana a kan ikon da Majalisar kasar  (iko da kuma alfarma)…. Babu wata hujja da za a binciki wani dan majalisa, ko Kakakin Majalisar Wakilai, ko kuma Shugaban Majalisar Dattawa, idan abin da suke yi na cikin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.”

Kan batun kasafin kudin da ake zaragin cushe, kakakin na mai cewa, “kundin tsarin mulki magana yayi a kan kiyasin kudin shiga da kuma abin da za a kashe, wadanda za a shirya a kuma gabatarwa majalisar kasa. Babu wani abu wai shi ‘Kasafin kudi’ a kudin tsarin mulki domin kasafin kudi doka ce.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng