Shika-shikan soyayya masu kyautata zamantakewa
Ga wasu shika-shikan soyayya wadanda a cewar masana, idan aka kiyayesu, za su kara dankon zamantakewa musamman a rayuwar aure.
1.Tafiya tare
Domin karin fahimtar juna yana da kyau mace ta nuna sha’awa a abin da abokin zama ke so. Misali, idan mai gidanki mai son kwallo ne, yana da kyau ki taya shi, haka mai gida idan ya san matarsa ma’abociyar karatun littafai ce, samu lokaci ka rika karanta mata kaima.
2.Mai da hankali
Mai da hankali a kan juna a lokacin da ake tare yana kara dankon soyayya, musamman a lokacin da kuke hira, ba abin haushi irin kana magana da mutum amma ka ga hankalinsa ba ya tare da kai.
3.KIRKI
Kyautatawa juna babban jigo ne a zaman tare, akwai hanyoyi da yawa da mace za ta kyautatawa mijinta haka shi ma miji ke da su.
4.Hakuri da fahimtar juna
Hakuri shi ne maganin zaman duniya, kuma zo mu zauna, in ji masu iya magana, zo mu bata ne, sai dai idan ba a zama bai yi nisa ba. Mace ta fahimci halin da mijnta ke ciki, shima ya fahimci halin da matarsa ta ke ciki a halin rayuwa, hakan zai taimaka zama ya dore.
5.Nunawa juna kauna
Yana da kyau mace ta rika taba maigida a waya yana wurin aiki da kalaman kauna, ko da sakon tes, haka shima lokaci-lokaci ya rika yi mata kalaman soyayya tamkar yanzu suka fara ganin juna, ko da sun yi shekaru da yin aure.
Asali: Legit.ng