Sarakuna 5 da suka fi iya kwalliya
Da kaji an kira sunan sarakunan gargajiya, abin dake fara zuwa zuciya shine irin kayayyakin gargajiyan da suke sanyawa don nuna ado.
A wasu lokuttan kayayyakin basa musu kyau. Amma dai akwai wasu fitattun sarakuna guda biyar da suka yi fice a fagen iya kwalliya.
1. Sarkin Ife
Sarki Adeyey Enitan Ogunwusi dan saurayi ne mai shekaru 40 da ya kasance kwararren dan kasuwa ne dake harkar kadarori kafin ya zama Sarki. Sarkin ya fito ne daga gidan sarautan Ife na Giesi, Sarki Adeyeye shine Sarki na 51 a masarautar Ife. Sananne ne a fagen iya kwalliya.
2. Sarki Fredrick Akinrutan
An haifi Sarki Fredrick shekaru 60 da suka gabata, kuma shine Sarkin masarautar Ugbo dake yankin Ilaje na jihar Ondo, kudu maso yammacin kasar nan. shima yana da sha’awar yin kwalliya da shiga manyan motoci.
3. Sarkin Onitsha
Alfred Nnaemeka Achebe shine sarkin masarautar Onitsha, kwarjininsa yasa kwalliyar sa ke burge jama’a balle ace ya sanya kayan sarautar sa na gargajiya.
4. Sarki Rilwanu Akiolu
Cikakken sunan Sarkin Legas shine Rilwan Babatunde Osuolale Aremu Akiolu I wanda aka nada a shekarar 2003, sai dai jama’a sun san shi da son shiga irin ta yaranta.
5. San Kano
Sarkin Kano Muhammadu Sunusu II, wadda aka fi sani da Sunusi Lamido Sunusi a zamanin da yake shugabantar babban bankin Najeriya-CBN. An nada shi ne a 8 ga watan yuni na 2014. Tun zamanin sa na aikin banki ya shahara wajen iya kwalliya.
Asali: Legit.ng