Abubuwa biyar da ya kamata ka sani na Paul Pogba

Abubuwa biyar da ya kamata ka sani na Paul Pogba

Paul Pogba sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya zamo dan wasa mafi tsada a duniya bayan kammala komawarsa kungiyar akan zunzurutun kudi da suka kai dala miliyan 131 daga Juventus.

Abubuwa biyar da ya kamata ka sani na Paul Pogba

Pogba dan shekaru 23 ya koma kungiyarsa ta asali inda ya fara kwallo wato Manchester a wani yanayi da ya girgiza duniyar kwallon kafa, kuma zuwansa Manchester zai kara ma gasar firimiya ta Ingila da za’a fara a karshen mako ban sha’awa.

Ga wasu abubuwa biyar da baka sani ba dangane da Pogba

1. yana da shahararrun abokai

A daidai lokacin da yake shakatawa a kasar Amurka, an hangi Pogba ya sauka a Otel daya da fitaccen mawaki dan kasar Canada, Drake. Haka nan shima dan wasannan Lukaku a Otel din ya sauka, kazalika dan wasan kwallon karfi Chad Johnson.

Abubuwa biyar da ya kamata ka sani na Paul Pogba
Lukaku

2. sananne ne a shafin Instagram

Pogba dan wasan tsakiyan Faransa na da mabiya sama da miliyan 6 da dubu dari 7 tun da ya bude shafi a kafar sadarwa ta Instagram a watan janairu na 2016, kuma ana sa ran mabiyan nasa zasu karu tun bayan komawarsa kungiyar Manchester United.

3. yan uwansa ma yan kwallo ne

Da alamar harakar kwallon kafa ta mamaye dangin Paul Pogba, dalili kuwa shine, ya da yayyu wadanda tagwaye Florentin da Mathias ne da suke harkar tamola a Faransa da Scotland. Florentin na buga ma kungiyar Saint Etienne na kasar Faransa, shiko Mathias yana bugawa kungiyar Patrick Thistle a Scotland. Tagwayen yan wasan na buga ma kasar su ta asali ne wasa, wato kasar Guinea

Abubuwa biyar da ya kamata ka sani na Paul Pogba

4.

Ana kiran Paul Pogba da lakabin sunan II Polpo Paul, wato Paul dorinar ruwa. Sa’annan lokacin da yake wasa a Manchester United shekaru hudu da suka wuce ana kiransa da suna Nelson Mandela saboda irin goyon bayan da yake yi wa kocin su na wancan lokaci Sir Alex Ferguson.

5. yayi babban bako a Ballon d’or

Pogba ya tafi da mahaifiyarsa zuwa taron bayar da kyautan gwarzon kwallon kafa na Ballon d’or inda a taron aka sanya shi daga cikin jerin yan wasan da suka fi iya taka leda a binciken hukumar FIFA, da haka Pogba ya zamanto dan wasa mafi kankantan shekaru da ya taba shiga jerin yan wasan, bayan Lionel Messi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng