Dan wasan Najeriya Utaka ya samu tsaiko
Tsohon dan wasan kungiyar Super Eagles dake wakiltar kasar Najeriya John Utaka ya samu tsaiko kasantuwar cinikin siyen sa da ya watse. A da dai dan wasan yana ta shirin komawa ne kungiyar kwallon kafa ta Ismaily daka kasar Egypt.
wakilin dan wasan dai Tekin Birinci shine ya bayyana haka a shafin sa na sada zumuntar zamani na Tuwita mai adreshin @tekinbirinci. Wakilin nasa yace: "John Utaka da kungiyar Ismaily basu cimma yarjejeniya ba. Yanzu haka yana a kasuwa ga duk wanda ke so."
Shi dai dan wasan mai shekaru 34 a yanzu ya taba buga wasa a kungiyar ta Ismaily a shekara ta 1999 inda ya taimaka mata wajen lashe kofin kasar na Egypt cup inda ya zura kwallaye 17 cikin wasanni 21 da ya buga.
![Dan wasan Najeriya Utaka ya samu tsaiko Dan wasan Najeriya Utaka ya samu tsaiko](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt6tbuji9lr8g.jpeg?v=1)
Daga bisani ne kuma sai ya tafi nahiyar turai ina ya buga kwallo a kungiyoyi da dama a kasar Ingila da ma Faransa ya kuma lashe kofuna da dama da shi din.
Asali: Legit.ng