Al'ajabi: Wata mata taga giza-gizai da siffar Yesu

Al'ajabi: Wata mata taga giza-gizai da siffar Yesu

Wata mata mai shekara 26 kuma da ya'ya 2 yace tayi matukar mamaki da yadda taga wani girjije mai siffar Yesu bayan da ta dauki sararin samaniya hoto da wayan ta.

Da take bada labarin yadda lamarin ya faru, matar mai suna Becky tace: "Ina cikin daukar hotuna na daga tagar dakin dana daf da faduwar rana sai kawai naga na dauki wani hoton girgije mai kama da fuskar Yesu. "Nan da nan ne kam sai na kara girman hoton don in kara tabbatar ma idona abunda na gani."

Al'ajabi: Wata mata taga giza-gizai da siffar Yesu

Daga nan ne sai matar ta turawa mahaifiyar ta hoton wadda abun yayi matukar bata mamaki ganin yadda hoton yayi kama da furkar Yesu sasai. Daga nan ne fa sai suka saka hotunan a kafafen sadarwar zamani. Ba a dauki tsawon lokaci ba da yin hakan kau sai hotunan suka watsu cikin duniya ina mutane suka cika da al'ajabin hakan.

Ita kuma Becky sai ta kara da cewa: "Ina ganin dai duk mai ido yaga abunda na gani. Hoto ne gashi nan kuru-kuru mutum ne da gemu kamar dai Yesu shiyasa ma nayi tunanin hakan." Wani labari ma dai mai kama dahakan wani abun mamaki ya faru a garin Makurdi dake jihar Benue inda mutane suke ta tururuwa a cocin katolika ta Saint Augustine don ganin wani hoto da ya bayyana a cikin ta da suka ce na Yesu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel