Wata mata ya sanya ma haifaffiyar cikinta guba
–Wata mata ta sanya ma yar ta mai wayanni 17 da haihuwa guba .
–Matan ta baiwa yarinyar zallan gishiri cikin cokali.
–Yarinyar ta mutu sanadiyar gubar gishiri kuma mahaifiyar zata kwashe shekaru 20 a gidan yari.
Wannan mumunan hadarin ya farune a birnin south Carolina a makon da ya gabata,yayinda wata mata yar shekara 23 ta aika haifaffiyar cikinta lahira da gangan.
Game da cewat rahotanni, Matan mai suna Kimberly martines ta baiwa yar jaririyar mai suna peyton cokalin gishiri kuma jim da kadan yarinyar ta fara figar ruwa. Da aka kaita asibiti domin taimaka ma rayuwarta likitocin asibiti suka ce ai kwakwalwanta ya riga ya mutu.
Yayinda ake magana akan kisan, lauyan Mrs Kimberly martines, Barry Barnette, yace : tayi hakanne domin dawo da mijin cikin rayuwarta ,domin jawo hankalin shi.
Dangin matan suke koka rasuwan peyton suka ce : bata kuka kuma tana sa kowa dariya.babu yanda zakayi kaki yin dariya idan kana kusa da ita. Wata yarinya ce wacce ke so koda yaushe a gyara mata farce kuma abinda tafi so shine minnie mouse.
KU KARANTA : Likita ya manta da tawul a cikin wata mata.
Akwai yiwuwan idan kotu ta kama martines da laifin cin zarafin yara. Zata kwashe shekaru 20 a gidan yari. Yara nada yiwuwan mutuwa daga gubar gishiri sabida kodar su bata girma sosai ba.
Asali: Legit.ng