‘Yar Denmark na gina gidan kula da marayu a Nigeria

‘Yar Denmark na gina gidan kula da marayu a Nigeria

Wata ‘yar asalin kasar Denmark waccce ta daukar wa kanta ceton yaran da aka yar saboda kazafin maita a jihar Akwa Ibom, ta soma gina wani katafaren gidan kula da marayu a jihar.

‘Yar kasar ta Denmark wacce ta ke auren wani dan Nigeria Anja Ringgren Loven, wacce kuma ta yi ficce wajen tallafawa yara marasa galihu, ta kuduri aniyar taimakawa yaran da aka watsar a jihar Akwa Ibom.

‘Yar Denmark na gina gidan kula da marayu a Nigeria
Anja da mijinta da kuma daya daga cikin yaran da ta ceto

Anja wacce ta ceto wani karamin yaro ta aka yar a gefen titi, a bisa zargin maita, ta kuma dauki nauyin kulawa da shi, ta kuduri niyar taimakawa irn wadannan yaran a jihar ta hanyar gina wani katafaren gidan marayu wanda a cewarta, zai taimaka wajen kula da yara kanana marasa galihu.

A wani bayani da ta lika a shafinta na sada zumunta da muhawara a Intanet, Anja ta ce; “….muna kan gina wasu gine-gine guda 6 daga cikin manya-manya da za mu yi, wadanda suka hada da dakunan kwana na maza da na mata, da dakin dafa abinci, da ofis-ofis da dakin karatu, muna sa ran kammalawa a ‘yan watanni masu zuwa… za kuma mu gina wani karamin asibiti da taimakon gwamnatin Denmark”.

Aikin Anja na ceto kananan yara daga hallaka bayan an  yar da su, da ‘yan asalin jihar ke yi, ya janyo mata farin jini a ciki da kuma wajen Najeriya, musamman a intanet a inda ta ke sa hotunan yaran da ta ceto.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng