‘Yan sanda sun gano tarin albarusai a ramin gini (Hotuna)
Rahotanni na cewa ‘yan sanda sun gano tarin albarusai da aka binne a wani rami a jihar Anambra.
‘Yan sandan sun gano tarin albarussan ne a yayin da ake haka fandishan gina wani gida a garin Agulu na jihar Anambra.
A hirarsa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sam Okaula, ya ce da bokiti aka rika kwaso tarin albarusan daga ramin ginin, a inda jami’an ‘yan sandan suka rika kwaso bokitai na albarusan da Allh ne kadai ya san yawan su daga ramin, ba a kuma gama kwashewa ba a lokacin da ya ke hira da ‘yan jaridun saboda yawansu.
Kwamishina ya ci gaba da cewa, an soma gudanar da bincike gadan-gadan domin gano lokacin da aka binne alabarusan, da wadan ya binne su, da kuma da dalilin da ya binne su a wurin.
Sannan ya yi kira ga jama a da su taimakawa rundunar da duk wasu bayanai da za su taimaka a gano bakin zaren a binciken da su ke yi.
Asali: Legit.ng