Yadda ake gane mai hikima

Yadda ake gane mai hikima

Ana iya haihuwar mutum da basira kuwa? Masana ilimin dan adam sun gano wasu abubuwa biyar da ka iya sanya mutum ya kasance mai basira da hikima.

Yadda ake gane mai hikima

A biyo mu a ji wasu abubuwa ne haka.

 Bahago

 Baiwa ne a haifi mutum bahago, bahagwaye sunfi saurin tunani wajen yanke shawara, sa’annan sunfi basirar kirkire kirkire.

 Ban dariya

 An gudanar da wani bincike tun a shekarun saba’una, kuma binciken ya nuna cewa mutane masu ban driya sunfi sauran mutane gama gari wayo, sa’annan sunfi saukin kai.

Yadda ake gane mai hikima

Dan fari

 Duk dan fari yana gadan hikimar iyayensa fiye da sauran yaya. A wannan zamanin ma haka abin yake, idan kaan da kannai toh sai ka dinga koyar dasu, a haka zaka karu.

 rashin jin barci da dare

 Masana sun gano cewa wadanda ke dadewa cikin dare ba tare da sun ji barci ba sunfi basira fiye da masu farkawa barci da sassafe. Zasu iya kasancewa masu arziki da kuma samun kwanciyar hankali.

Yadda ake gane mai hikima

mai zurfin ciki

 Kasha 60 na mutane masu tsananin hikima suna da zurfin ciki. Ko mai haka ke nufi? Zurfin ciki shine dogaro da kai ba tare da sauraron mutane ba. Misali a ce mutum da kansa ke samar ma kansa mafita, ba tare da ya tambayi wanin sa ba.

Idan kana da daya daga cikin alamun nan, tabbas zai iya kasancewa kafi sauran abokan ka hikima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel