‘Yan Shi’a ba Musulmai bane  - Majalisar koli ta Shari’a 

 ‘Yan Shi’a ba Musulmai bane  - Majalisar koli ta Shari’a 

 

–An siffanta Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN),wadanda akafi  sani da yan shi’a a matsayin bara gurbin musulmai

“Muna kokarin fadakar da mutane cewan shi’a ba musulunci bane, abinda sukeyi ba musulnci bane.

–Majalisar koli ta shari’a ta kuma ta ca da kungiyar kistocin najeriya,shiyar arewa da kokarin cuta kiyayyan musulmai zukatan Kirista.

Hakazalika , Majalisar koli ta shari’a ta siffanta Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN),wadanda akafi  sani da yan shi’a a matsayin bara gurbin musulmai kuma ayyukan su ya sabawa addinin musulunci. Majalisar kolin ta kuma yi kira da shugancin jihar kaduna ta aiki da binciken da aka bata. Kana tayi dubi akan maganan da kungiyar kiristocin najeriya CAN tayi.

 ‘Yan Shi’a ba Musulmai bane  - Majalisar koli ta Shari’a 
(IMN)

Shugaban majalisar, Sheik Yusuf Sambo Rigachikun, mataimakin shugaban majalisar, Sheik Muhammad Suleiman , sun yi bayanin matsayar majalisar kolin a taron da aka yi a Kaduna a ranar lahadi.yace : “Muna kokarin fadakar da musulmai cewa shia’a ba musulunci bane ,abunda suke ikirari ba musulunci bane , suna zagin sahabbai, matan manzon Allah ﷺ wanda ke nuna wannan ya sabawa musulunci.

Yayinda yake Magana akan abinda ya faru a zariya, wata hayaniya da aka samu tsakanin rundunar sojin najeriya da yan shi’a a watan disamban 2015, sun wanke sojoji kuma an daura aifi akan yan shi’a. Yayinda yake Magana akan kiran da kungiyar CAN shiyar arewa take cusawa mabiyanta, y ace : “ kiristoci su sani cewanajeriya tamu ce gaba daya, dukan mu yan najeriya ne. Muyi kokari mu zauna lafiya , cewa kowani kirista ya tanadi makami abune wanda bai dace ba kuma ba’ayi neman zaman lafiya ba.

KU KARANTA : Iran ta matsa kaimi a kori Burutai

Kuma, yan shia tace jami’an tsaro na shirin kama mambobin ta da ke hanyar zuwa Abuja domin zanga-zangan neman sakin shugabansu ,Sheik Ibrahim Zakzaky. A wata jawabin da shugaban yada labarum shian ya fada, yace : “ shirin na kokarin kai hari ga matasa masu zuwa Abuja a tare da makamai ba amma ace an kama su da makamai. Sannan jami’an tsaro suyi gaggawan cewan yan shi’a na kokarin kawo hari Abuja . muna son mu sanar da jama’a cewa wannan samarin a zanga zanga cikin lafiya da lumana.

Zaku tuna cewa a disamban 2015, rundunar sojin naje sun kai farmaki gidan Ibrahim zakzaky a zaria, sun kasha daruruwan mutane  kuma shi shugabansu na daure a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng