Tsabar soyayya dake tsakanin Obama da yayansa (hotuna)
Sanin tsakanin uba da ya abu ne mai wuya. An sani cewa yaya mata na shakuwa sosai da iyayensu maza.
Idan aka kula za’a gane cewa Uba na daukan yarsa da muhimmanci sosai, ba wai yaya mata basa son iyayensu mata bane, a’a, sai dai sun fi shakuwa da mazan ne.
Kasancewar namiji Uba ba karamin aiki bane, don haka ne ma yaya mata ke kaunar iyayensu maza don suna samun karbuwa daga wajen su, sa’annan hakan na kara musu kwarin gwiwa a wajen karatun su. shugaban kasar Amurka Barack Obama na da yaya mata biyu wadanda suke kallonsa a matsayin abin koyi. Soyayyar dake tsakanin sa da yayan nasa shine misalin kololuwar soyayyar dake tsakanin Uba da ya.
Za ayi mamaki idan ake ce Obama na gudanar da hakkokinsa na Uba duk da irin tarin ayyuka dake gabansa na shugabancin kasar Amurka, yana kulawa da iyalinsa matuka. Ga wasu hotuna da ka iya burge mai karatu dake nuni da irin dangantakar da ka iya kasancewa tsakanin Uba da yaya mata. Ga wasu daga cikin hotunan Obama da iyalinsa.
1. Soyayyar Uba ya dara komai
Duk da irin tarin hidimomin da ke gaban shugaba Obama, amma yana kokarin baiwa yayansa lokacinsa. A wurin Obama, iyalinsa sune abin kulawa na farko. Da fatan wannan zai sa iyaye maza sun dinga samun lokaci suna zama da iyalinsu a gida
2. abin sha’awa
Yayan Obama na da kyau matuka; ya kan fita su lokaci zuwa lokaci, da alamar kasancewarsa shugaban kasar Amurka bai kai kasancewarsa uban yayan nasa dadi ba.
3. Obama tare da babbar yarsa
4. Iyalin Obama
Rayuwar na zama mai inganci idan ana samun ire iren wannan haduwar. Yaya mata sunfi samun kwanciyar hankali idan suna yawan ganin babansu a gida. Su kan iya fadi masa duk damuwarsu, shi kuma ya magance musu ita.
5. bikin kirsimeti tare da iyali akwai dadi
Tabbas shugaba Obama yana kulawa da iyalinsa, dubi yadda yayansa ke kallonsa.
6. kalli abin birgewa
Wasu iyaye maza na gazawa ne idan suka kasa bambamcewa tsakanin aikinsu da kuma iyalinsu. Duk da irin muhimmancin da duka biyun suke da shi. Yaya mata sunfi girmama babansu idan suna yawan kasancewa tare da shi, kuam baban zai dinga nuna musu yadda rayuwa take.
7. tsohon hoton Obama da yayansa
Wannan gwanin kyau ne, samun lokaci da yaya mata zai kara dankon zumunci tsakanin ubansu da su.
8. Obama rike da hannun yarsa
Idan yarinyar na tare da babanta, hakan zai kara mata kwazo, wannan shi ke nuna tabbacin kauna. Uba shine mutumin da yarinya ke fara so.
9. sauran iyaye su dage da zama kamar Obama wanda ked a fada a ji a siyasar Amurka, sa’annan kuma iyalinsa na girmama shi a matsayin sa na Uba da miji.
10. Uba na gari
Daga wadannan hotunan, za’a fahimci cewa shugaba Obama na kulawa da iyalinsa kuma yana kaunar yayansa, yana kokarin share musu hawayensu duk da hidimar mulki dake gabansa.
Asali: Legit.ng