Illolin sa hotunan yara barkatai a Yanar Gizo
Kamata iyaye su karanta wannan kafin su lika hotunan ‘ya ‘yansu a shafukan sada zumunta da muhawara na Intanet.
Abin murna ne da alfahari iyaye su lika hotunan ‘ya ‘yan su kanana a shafukan sada zumunta da muhawara na Istagram ko Facebook ko Twitter da sauransu, sai dai ba kowanne hoto na ‘ya ‘yanka kanana ya kamata ka sa a wadandan shafukan ba a bisa wadannan dalilai guda 8.
1. Hotunan yara a tube
Intanet na da fadi, ta na da kuma girma, hotunan yara a tube kamar lokacin da suke wanka ko wasan a ruwa ba na ganin kowa da kowa ba ne, da akwai bata gari.
2. Rashin lafiya
Idan kana da dabi’ar daukar hoton yara da kuma sa wa shafinka na intanet, ya kamata ka daina.
3. Kunya
kwarrarru a kan kimiyyar halayyar dan adam sun yi ittifakin cewa, sa hotuna da za su kunya yaro a intanet a matsayin horo, na haifar da mummunar sakamakon a rayuwarsa a gaba.
4. Ban daki
Ya kamata iyaye su tambayi kan su, shin yaya yaron zai ji idan ya ga wannan hoto bayan shekaru kimanin 10 ko 20? Aiki da hankli dai ya fi aiki da agogo kafin ka yadawa duniya.
5. Cikakkun bayanin yara
Ba kowanne bayani na kashin kai ake sa wa a shafukan sada zumunta ba, don haka a kiyaye cikakkun suna da addireshi kuma zirga-zargar yara, don gujewa fadawa hannun masu satar yara da ire-irensu.
6. Hotunan yara tare da ‘yan uwansu
Shin sauran iyaye sun aminice da ka sa hotunan ‘ya ‘yansu da suka dauka da naka a shafinka na intanet? Bisa doka, za su iya kai ka gaban kuliya.
7. Hotunan ban barakwai
A guji sa hotunan yara a wani hali na daban, za su iya zama abin tsokana da takuwara daga abokansu
8. Hotunan hadari
Hotunan yara a halin hadari, na iya jefa ka cikin hadari kai ma.
Asali: Legit.ng