Bayan Sunyi Fada,Matar Ta Bar mijinta,Amma Yayi Rubutu kamar haka. 

Bayan Sunyi Fada,Matar Ta Bar mijinta,Amma Yayi Rubutu kamar haka. 

Farkon labarin ze saka rudani,wani miji ya dawo gida bayan tashi aiki da gajiya,sai ya fara kallon talabijin, ita kuma matar tana kokarin shinfidar da yaransu. Mijin da yake cikin jin haushi da gajiya,wanda ya ke tunanin ya gaji da abubuwan da ke faruwa ,ya kara daga muryar abin kallon dan kada yaji kukan yaran.

Ana haka matar ta fusata, kawai sai suka fara cece-kuce,ta goranta ma mijin akan baya taya ta gurin kula da yaran,mijin ya tsagal-gale akan bata komai kullum in ya fita aiki. Daga karshe ,matar tana kuka ta tafi gidan iyayenta,bayan kwana 2 mijin a aiko ma matar takarda kamar haka.

KU KARANTA : Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

 "Masoyiya ta, Kiyi hakuri da hali na,yayin da kika tafi,nayi tunanin abinda ya faru,da abinda yake daukar mace ta zama uwa. Nayi kokarin sa yara bacci,da kyar na samu suka yi,da naga baki dawo da safe ba, na dauki hutun kwana 1,nayi duk aika-aikacen da kike,ina cikin hidima a ko yaushe, ban samu lokacin zama ba balle hutu. Banda wani aiki sai dafa abinci,ci da yara,canza masu kaya,gyara gida.Akwai lokacin da wasu abubuwa tare nake yinsu. Ina cikin gida ban samu damar lekawa ko waje ba, ban samu damar magana da kowa ba,yanzu na gano sadaukar da lokacin ki da kike yi da kula da yara ,haka ya faru rana ta 2,saboda haka na gano abubuwa da yawa kuma na gane kuskure na. Na gane kasancewa uwa sadaukar waa ce,sanna kasancewa uwa ya fi zama ofis na awa 10,na gano kasancewa uwa shine aiki da yafi komai,amma yawanci ba aba hakan mahimmanci,kuma ba'a yabon haka. Narubata wannan wasikar ba dan kawai ince kiyi hakuri ba kuma ba dani ince nayi kewar ki ba,ina so ina fada maki mahimmancin a ko da yaushe,ke jaruma ce, ke ce farin cikin iyalina. Ina Kaunar ki.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel