Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa

Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa

Wata mata mai suna Rose Geil ta kasance tana da gemu sosai a fuskarta da har ya kai ga tana jin kunyar gashin, inda take aske shi akai akai.

Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa
Rose

Wannnan mata shekarunta 39, kuma ta kwashe shekaru 26 tana fama da wannan lamari. Tun kuruciyarta Rose ke kokarin tabbatar da yanayin ta na mace ta hanyar yawan aske gashin, tanada baiwar gashi ba a fuskarta ba kadai, har ma hannayenta da sauran sassan jikinta. Daga karshe dai ta hakura da yawan aske asken, ta rungumi kaddara.

Rose ta fara shiga yanar gizo tana bayyana kanta, kuma tana alfahari da kanta. Daga sai samari da yawa suka dinga nuna sha’awar kulla alaka da ita, ita ko Rose bata yi mamakin hakan ba.

Tace “ban yi wani mamaki ba, nasan dole akwai ire iren mutane da hakan ke burge su”

Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa

Ko menene dalilin da yasa gashi ke fito mata haka sosai a jiki? Masana sun ce ana samun irin wannan lamari ne a jinni, tana dauke da wani sinadari mai suna Polycystic Ovary. Yarinyar ta nuna juriya ba kadan ba dangane da tsokana da nuna wulakanci.

“na fahimci irin jama’ar da nake bukatan zama da su tun kafin in bari gemun ya fara fita, na dade ina bin kadin labarin mata masu gemu, wadanda siffarsu bata yi kama da ta kow ba. Anan na samu kwarin gwiwa, abune mai kyau.Muna bukatan a fahimce mu, kuma a nuna mana kauna, amma fa tabbas irin siffar mu na hana mu shiga wasu al’amuran cudedeniya da mutane.”

 

Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa
Mace mai gemu, mai zawarawa da yawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel